Manyan hafsoshin tsaro da gwamnonin arewacin Najeriya sun gana kan satar mutane

Sakamakon yawaitar matsalar satar mutane a Najeriya, gwamnonin arewacin ƙasar sun amince da yin haɗin gwiwa da gwamnatin tarayya da kuma duba yiyuwar yin amfani da wasu hanyoyin na daban wajen shawo kan ƙaruwar matsalar taɓarɓarewar tsaro da take addabar yankin arewa.
An cimma waɗannan shawarwari ne a yayin wani taro da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya ƙira tsakaninsa da ƙungiyar gwamnonin arewacin Najeriya da manyan hafsoshin tsaro ciki harda Babban Sufeton ‘yansanda da kuma kwamandan Rundunar Tsaron Sibil Difens.

An shafe fiye da sa’o’i 4 ana gudanar da taron wanda ya gudana cikin sirri sa’annan bayan kammala shi Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa, gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gwambe ya yi ƙarin haske game da abubuwan da aka tattauna akai.

Ya kuma bayyana shirin ƙungiyar gwamnonin ta yin amfani da wasu hanyoyi na daban wajen shawo kan taɓarɓarewar tsaro a arewacin Najeriya.

Gwamnan ya ƙara da cewar za’a nemi gudunmawar sojoji wajen murƙushe masu ta da ƙayar baya ba tare da yin amfani da ƙarfi ba.

“Kamar yadda kuke gani, wannan taro ne tsakanin gwamnonin arewacin Najeriya da manyan hafsoshin tsaro da kuma mashawarcin shugaban ƙasa akan harkokin tsaro”.

Ya ci gaba da cewar, “wannan taro ne da ya shafi tsaro, kuma kun san irin muhimmancin da tsaro ke da shi, musamman ma yanzu da matsalar yin garkuwa da mutane ke ƙara ƙaruwar a shiyyar arewa maso yamma, don haka akwai buƙatar mu tattauna mu sake nazari tare da rungumar wasu dabarun na daban akan waɗanda muke yi domin samun mafita”.

KU KUMA KARANTA:An tsare ɓarayi 2 kan satar buhun zoɓo 10 a Jigawa

A makon da ya gabata ne , ‘yan bindiga suka sace kusan ɗalibai 300 daga wata makaranta a ƙauyen kuriga da ke ƙaramar hukumar chikun ta jihar kaduna.

A wani taron manema labarai na daban, sojoji sun sha alwashin kuɓutar da dukkan waɗanda ake garkuwa dasu.

Game da satar ‘yan gudun hijra a garin gamborun ngala na jihar borno kuma, sojojin sun bayyana cewar mutanen sun zartar tazarar da aka amince su je daga sansaninsu.

Haka kuma, daraktan yaɗa labaran ma’aikatar tsaro, manjo janar edward Buba, ya ce samun jinkiri wajen kai rahoton satar mutane na kaiwo tsaiko wajen kai ɗaukin gaggawa daga hukumomin tsaro da sauran jama’a.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *