Maniyyata 200 kacal suka biya kuɗin hajji a Taraba

0
20
Maniyyata 200 kacal suka biya kuɗin hajji a Taraba

Maniyyata 200 kacal suka biya kuɗin hajji a Taraba

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ware wa jihar kujeru 1,400 domin maniyyatan jihar domin sauke farali a bana, amma mutum 200 kacal suka biya.

Wannan shi ne adadi mafi ƙaranci na maniyyatan aikin Hajji daga jihar.

KU KUMA KARANTA:Hukumar NAHCON ta sanar da kuɗin kujerar Hajjin 2025

Kakakin Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Taraba, Hamza Baba Muri, ya bayyana cewa a bara alhazai 1,007 me suka yi aikin Hajji daga jihar.
Ya ce saboda ƙarancin maniyyatan da suka kammala biyan kudin kujera, hukumar za ta gudanar da gangami a faɗin jihar domin ba wa jama’a ƙwarin gwiwa su biya.

A cewarsa, jami’an hukumar za su karaɗe ɗaukacin ƙananan hukumomin jihar domin wannan aikin neman ƙarin maniyyata.

Leave a Reply