No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar jin Daɗin Alhazai ta jihar Kano ta ce aƙalla maniyyatan jihar 156 ne za su rasa aikin hajjin bana.

Hakan ya faru ne sakamakon sayar da kujeru fiye da yadda aka ƙayyade da tsoffin jami’an hukumar da gwamnatin jihar ta dakatar suka yi.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai, Darakta Janar na hukumar, Laminu Rabiu ya ce hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON ta ware wa Kano kujeru 6,144, amma jami’anta sun sayar da ƙarin kujeru 156.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar likitocin NAHCON ta koka da halartar mata masu juna biyu a Hajjin bana

Ya bayyana cewa za a binciki jami’an da suka aikata wannan laifi tare da gurfanar da su a gaban kotu, bayan kammala aikin Hajji bana.

Daraktan ya kuma yin ƙira ga waɗanda abin ya shafa da su yi haƙuri, tare da alƙawarta musu cewa za a sanya su a cikin sahun farko a aikin Hajji mai zuwa.

Ya zuwa yanzu Hukumar jin Daɗin Alhazan ta Kano, ta yi jigilar maniyyata 2,558, zuwa ƙasa mai tsarki.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

1 COMMENT

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...