Manchester City ta lashe Firimiyar Ingila sau huɗu a jere
Manchester City ta lashe Gasar Firimiyar Ingila bayan ta lallasa West Ham da ci 3-1 a wasan ƙarshe na kakar bana da suka fafata a filin wasa na Etihad.
Phil Foden, wadda ya lashe lambar yabon gwarzon ɗan wasar kakar bana ne ya zura kwallaye biyu a mintuna na 2 da na 18.
Sai dai jim kaɗan kafin tafiya hutun rabin lokaci, Mohammed Kudus ya rama wa West Ham kwallo ɗaya a minti na 42 da buga wasan.
Mintuna 14 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci City ta sake ƙara kwallo ɗaya ta hannun ɗan wasan tsakiyarta, Rodri a daidai minti na 59 na wasan.
KU KUMA KARANTA: Yadda Arsenal za ta iya lashe Firimiyar Ingila
A wasannin na yau ne da aka fidda zakarar gasar ta bana, bayan an yi tafiya kafada da kafata tsakanin Manchester City da ƙare da maki 91, yayin da Arsenal ta ƙare a matsayi na biyu a teburin gasar da maki 89.
Wannan shi ne karo na farko a tarihin Firimiyar Ingila da wata ƙungiya ta lashe gasar sau huɗu a jere.