Man fetur da ake sha a Najeriya ya ragu da kashi 35

2
280

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, (NMDPRA) ta ce yawan man da ake amfani da shi a ƙasar a kowacce rana ya ragu zuwa lita miliyan 46.34, sakamakon cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

Shugaban hukumar, Ahmed Farouk, ne ya bayyana haka a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan harkokin albarkatun man fetur da iskar gas a birnin Legas, kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar (NAN) ya ruwaito.

Ya ƙara da cewa raguwar ta kai kashi 35 cikin 100 idan aka kwatanta da lita miliyan 65 da ake amfani da shi a kowacce rana kafin cire tallafin man fetur ɗin.

KU KUMA KARANTA: Majalisar Wakilai za ta binciki dalilin ƙaruwar farashin man fetur a Najeriya

Ahmed Farouk ya ce ”a watan Janairu fabrairu, an sha mai lita miliyan 62 a kowacce rana, yayin da aka sha lita miliyan 71.4 a kowace rana cikin watan Maris, sai Afiru da aka sha lita miliyan 67.7 a kowacce rana, sai watan Mayu da aka sha lita miliyan 49.5 a kowace rana, sai kuma watan Yuli da ake shan lita miliyan 46.3 a kowace rana”.

Shugaban hukumar ya kuma gode wa ‘yan kasuwar da suka nuna sha’awarsu wajen shigar da man fetur ƙasar daga kasuwannin duniya.

Ya ƙara da cewa kawo yanzu kamfanoni 56 ne suka nuna sha’awarsu wajen shigo da man fetur zuwa ƙasar, yayin da kamfanoni 10 suka zaƙu wajen fara shigo da man.

Ahmed Farouk ya ce yanzu haka kamfanoni uku sun fara shigo da man fetur ɗin daga ƙasashen waje.

2 COMMENTS

  1. Hakikanin gaskiya dole ya ragu, zakaji da cin abinci ne ko kuma sanyawa mota ko mashin dinka fetur?
    Rayuwa tayi tsanani ga yan Najeriya, yanzu kasamu ka rayu ma ba karamin babbar nasara bane.
    Ance tallafin man fetur wasu yan tsiraru ne ke cinye kudin suna azurta kansu, an wofintar da yan najeriya an sanya masu tsanar tallafin Mai, yanzu anyi walkiya kowa ya tabbatar cewa maganan wai ‘yan tsiraru ke cinye kudin tallafin man fetur karya ce; mu talakawan mune muke amfana dashi.
    Allah yakawo mana saukin rayuwa yakuma sanya tausayin mu a zukatan shuwagabannin mu.

Leave a Reply