Makaho ya damfari wata mata naira miliyan 19, ya yi lalata da ‘yarta da jikarta

0
339

Wani makaho mai suna Owolabi Adefemi da aka fi sani da Ojunu ya damfari wata mata ‘yar shekara 86 mai suna Madam Alimot tare da yin lalata da ‘yarta da jikarta a jihar Ogun.

Jaridar Alfijir Labarai ta rawaito an yi zargin cewa mai ba da maganin, na sayar da magunguna ganyaye inda ya yaudare ta zunzurutun kuɗi da nufin samar da waraka ga ‘yarta da ke fama da rashin lafiya.

Ƙarin cikakkun bayanai masu tayar da hankali sun nuna cewa Adefemi ya yi lalata da ‘yar Alimot, Bose, da kuma jikarta.

Uwargida Alimot, da ke Mowe a jihar Ogun, ta gano wanda aka ce mai maganin gargajiya ne bayan ta ji tallan sa a wani gidan rediyon jihar Ogun, inda aka yi masa bushara da basirar sa na sihiri na warkar da cututtuka da kuma hasashen abubuwan da za su faru a rayuwa, inda matar ta garzaya ga dan-duban a Ogijo domin samun mafita, inda rahotanni suka tabbatar da cewa Alimot ta sayar da gine-ginenta guda biyu don biyan waɗannan buƙatu.

KU KUMA KARANTA: Wani ɗan Sakkwato ya damfari mutane 12 kuɗi har naira miliyan 325

Bose, ɗiyar Alimot, ta amsa laifinta cewa sun yi kwanciyar aure da Adefemi, kuma ta yi ƙarin haske game da halin da take fuskanta.

“Daga baya Baba Ojunu ya gargaɗe mu da ka da mu gaya wa kowa abin da ya faru tsakanin mahaifiyata da shi, inda ya yi barazanar cewa za mu rasa rayukanmu idan ba mu yi biyayya da gargaɗin nasa ba,” Bose ta bayyana.

Adefemi da ke ƙoƙarin rage girman badaƙalar da ya ke yi, ya ce ya damfari Madam Alimot sama da Naira miliyan biyar ne kawai ba wai naira miliyan 19 da ake iƙirari ba.

“Na kasance ina yaudararsu cewa wani aljani na magana da Mama game da halin da take ciki.

Abin da Mama ba ta sani ba, ni ne nake yin ƙaryar muryar wata tsohuwa don in yaudare ta,” inji bokan.

Al’amarin ya bar iyalin cikin ɗimbin basussuka, da fuskantar bala’in da ya biyo bayan aukuwar lamarin.

Yanzu suna neman adalci, a mayar musu da kuɗaɗensu, kuma suna fatan wayar da kan al’umma game da yaudarar mutane irin ta su Adefemi.

Leave a Reply