Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ƙudurin samar da ƙasar Falasɗinu

0
192
Majalissar Ɗnkin Duniya ta amince da ƙudurin samar da ƙasar Falasɗinu

Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da ƙudurin samar da ƙasar Falasɗinu

Daga Jameel Lawan Yakasai

Majalisar Dinkin Duniya ta amince da wani kuduri da ke kira da a samar da ƙasar Falasɗinu tare da Isra’ila domin kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe a Gabas ta Tsakiya. Kudurin ya kuma yi kira ga ƙungiyar Hamas da ta kawo ƙarshen mulkinta a zirin Gaza.

A cikin zaman da aka gudanar, ƙasashe da dama suka goyi bayan kudurin, sai dai Isra’ila da Amurka da wasu ƙasashe tara ne suka kada kuri’ar adawa da shi. Wannan ya sake bayyana rarrabuwar ra’ayi tsakanin ƙasashen duniya kan mafita ta siyasa ga rikicin Falasɗinu da Isra’ila.

KU KUMA KARANTA: MƊD ta amince da ci gaba da shirin wanzar da zaman lafiya a Lebanon

Kudurin ya sake jaddada muhimmancin tattaunawa da hanyoyin diflomasiyya wajen tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin. Wannan batu na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun tashin hankali da rikice-rikice a Gaza da Kogin Yordan.

Leave a Reply