Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da rahoton haɗe hukumomi a wuri guda

Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da aiwatar da wani sashe na rahoton kwamitin Stephen Orasanye kan haɗa wasu hukumomin da ma’aikatun gwamnati a wuri guda, a yayin da wasu kuma za’a sauya musu fasali ko kuma a rushesu sannan wasu kuma a sauya musu matsugunai.
An cimma wannan matsaya ne a yayin zaman Majalisar Zartarwa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a yau Litinin.

Hakan, a cewar Hadimar Shugaban ƙasar akan aiwatar da manufofi, Hadiza Bala Usman, ya dace da buƙatar rage kashe kuɗaɗe wajen gudanar da gwamnati tare da inganta ƙwazo a dukkanin matakan aikin gwamnati.

Haka kuma, Majalisar Zartarwa ta karɓi rahoton Kwamitin alaƙa tsakanin Ma’aikatun Gwamnati da aka kafa domin sake nazarin tallafawa al’umma na ƙasa.

Har ila yau, Majalisar Zartarwa ta amince da sake farfaɗo da shirin baiwa iyalai miliyan 12 tallafin kudade kai tsaye da suka ƙunshi ‘yan Najeriya miliyan 60 dake da matuƙar buƙata.

A shekarar 2011, Shugaban Ƙasar wancan lokacin Goodluck Jonathan, ya kafa kwamitin sauya fasali da daidata hukumomi da ma’aikatun gwamnati ƙarƙashin jagorancin Oransaye.

KU KUMA KARANTA:Wata mata ta ɗauki nauyin kuɗin makarantar masu koyon aikin haɗa magunguna a New York

A ranar 16 ga watan Afrilun shekarar 2012, kwamitin ya gabatar da wani rahoto mai feji 800 da ya tantance ɗimbim hukumomin da ayyukansu ke kamance da juna abin da ke haddasawa gwamnati asara wajen kashe kuɗaɗe.

A cewar rahoton akwai hukumomi da ma’aikatun gwamnati 541, tare da ba da shawarar rage hukumomi 263 su koma 161, a rushe 38 a kuma haɗa 52 a wuri guda.

An samu gabatar da ƙuduriri ba tare da aiwatar da wani abin a zo a gani ba ƙarƙashin shekaru 8 na Shugaban ƙasa Muhammad Buhari, saidai aiwatar da rahoton ya yi daidai da muradan sabuwar gwamnatin da ta gajeshi a ƙoƙarin ta na rage yawan kashe kuɗaɗe.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *