Majalisar wakilan Najeriya ta bawa jama’a haƙuri kan tsadar rayuwa

0
138

Majalisar Wakilan ƙasar ta bawa jama’a haƙuri kan matsalar tsananin rayuwa da sha’anin tattalin arziƙi ya sa ake fama da shi, inda ta sha alwashin magance lamarin cikin gaggawa.

Shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas ya bayyana wa taron manema labarai na mussaman cewa, sanin halin da jama’a ke ciki ya sa dole su ɗauki matakan gaggawa na magance yunwa da hauhawan farashin kayayyaki da suke ƙara sa ƙunci a rayuwar jama’a.

Ko da yake bai faɗi takamaiman lokacin da za a fara shimfiɗa tabarmar sauƙin ba, Tajudeen ya ce za a ɗauki mataki nan ba da daɗewa ba, domin buƙatar yin haka.

Kakakin Majalisar Wakilan ya jaddada cewa, Majalisa za ta ci gaba da ɗaukar matakai kan batutuwan da suka jiɓanci yalwar abinci da kuma sha’anin tsaro yadda manoma za su iya komawa harkar noma kamar yadda aka saba.

KU KUMA KARANTA:Alƙawuran NLC ba za su cika a lokaci guda ba — Gwamnatin Tarayya

Tajudeen ya ce lokaci ya yi da Majalisar za ta fara hukunta manyan jami’an tsaron da suka kasa iya riƙe amana ta ƙasa.

Bisa ga cewarsa, Majalisar na sane da ƙalubalen tattalin arziƙi da ‘yan ƙasa ke fama da shi, kuma tuni su ka fara ɗaukar matakai a wannan fanin inda ya ce sun himmatu wajen shawo kan koma bayan tattalin da mayar da ƙasar kan turbar ci gaba mai ɗorewa. Tajudeen ya ce batun ƙarancin abinci da ake fama da shi yana zuciyar sa domin samar da abinci shi ne abu mai muhimmanci ganin cewa rashin abinci yana da alaƙa da harkar tsaro.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umurnin a fito da hatsi iri daban daban har ton dubu 42, na masara, gero da sauran kayan masarufi a cikin tsare tsare don magance tashin farashin kayan abinci a ƙasar.

Leave a Reply