Majalisar Dokokin Kano ta amince da naɗa AVM Ibrahim a matsayin kwamishinan tsaron cikin gida
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da naɗin AVM Ibrahim Umaru (Rtd) a matsayin Kwamishinan tsaron cikin gida kuma mamba a Majalisar Zartarwar Jihar Kano.
Shugaban masu rinjaye na majalissar Lawan Hussaini Dala yace sun amince da nadin da Gwamna Abba Kabir yusif ya yiwa AVM ibrahim Umaru Duba da kwarewarsa wajen harkokin tsaro.
KU KUMA KARANTA:Kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na Kano ya ajiye aikinsa
Hon Dala ya Kuma buƙaci AVM Ibrahim Umaru da ya cigaba da jajircewa kamar yadda suka sanshi da ita wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.









