No menu items!

Sample Page Title

Date:

Majalisar Dattawa ta amince da naɗin sabbin hafsoshin tsaron Najeriya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da naɗin sababbin hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar a ranar Juma’ar da ta gabata. Wannan mataki na zuwa ne bayan tantancewa da tattaunawa mai zurfi da majalisar ta gudanar da su yau Laraba.

Wadanda aka amince da su sun haɗa da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Waidi Shaibu a matsayin Hafsan Sojan Ƙasa, Rear Admiral Idi Abbas a matsayin Hafsan Sojan Ruwa, da Air Marshall Kennedy Aneke a matsayin Hafsan Sojan Sama.

KU KUMA KARANTA: Sanatocin Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga al’ummar Falasɗinu a zauren majalisar dattawa

A yayin zaman tantancewar, sabbin shugabannin rundunonin sun gabatar da tarihin ayyukansu da gogewarsu a harkar tsaro, tare da amsa tambayoyi daga ‘yan majalisar kan hanyoyin da za su inganta tsaro da tabbatar da zaman lafiya a ƙasar.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...