Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu na naɗa masu ba da shawara na musamman guda 20

Majalisar dattawa ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Bola Tinubu na naɗa mashawarta na musamman guda 20.

Buƙatar shugaba Tinubu na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta a zauren taron ranar Talata.

Bayan karanta wasiƙar, shugaban majalisar dattawa, Ibrahim Gobir, APC – Sokoto East, ya ce “Majalisar ta yi la’akari da buƙatar.

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattijai, Philip Aduda ne ya goyi bayan ƙudirin, bayan nan ne majalisar ta amince da shi.

KU KUMA KARANTA: Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar kare haƙƙin yara

Sai dai shugaban bai sanya sunayen masu ba da shawara ga wasiƙar da Lawan ya karanta ba.

Wannan shi ne karon farko da Tinubu ya buƙaci da a amince masa ya naɗa muƙamin siyasa a Majalisar ƙasar tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.


Comments

One response to “Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu na naɗa masu ba da shawara na musamman guda 20”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Tinubu na naɗa masu ba da shawara na musamman guda 20 […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *