Jakadiyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield, ta ce Amurka ba za ta goyi bayan ƙudurin ba a yadda aka tsara shi.
Akwai yiyuwar kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya mai mambobi 15 zai kaɗa ƙuri’a a ranar Talata kan buƙatar ƙasar Algeria ta neman a tsagaita wuta a yaƙin Isra’ila da Hamas ba tare da ɓata lokaci ba, a cewar wani jami’in diflomasiyya, wani mataki da Amurka ta nuna alamar za ta hau kujerar na ƙi.
Makonni biyu da suka wuce ne ƙasar Algeria ta gabatar da daftarin ƙudurin farko. Amma Jakadiyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta ce rubutun daftarin ƙudurin na iya kawo cikas ga” muhimmiyar tattaunawar” da ake yi da nufin yin sulhu a yaƙin.
KU KUMA KARANTA:Majalisar wakilan Najeriya ta bawa jama’a haƙuri kan tsadar rayuwa
A ranar Asabar ne Algeria ta buƙaci kwamitin sulhun majalisar ya kaɗa ƙuri’a a ranar Talata, in ji jami’an diflomasiyya. Don ya samu karbuwa, ƙudurin Kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya na bukatar akalla kuri’u tara dake goyon bayansa, kuma babu daya daga cikin kasashen Amurka, Birtaniyya, Faransa, China ko Rasha da zasu ki amincewa da shi.
“Amurka ba ta goyon bayan daukar mataki kan wannan daftarin kudiri. Idan har ya kai ga matakin kada kuri’a kamar yadda aka rubuta shi, ba za mu amince da shi ba,” in ji Thomas-Greenfield a wata sanarwa a ranar Asabar.
Dama Amurka ta kan kare abokiyar huldarta Isra’ila daga matakin Majalisar Dinkin Duniya, kuma sau biyu ta na yin watsi da matakin majalisar tun daga ranar 7 ga Oktoba. Amma kuma sau biyu tana daga kafa, abin da ya ba majalisar damar aiwatar da wasu kudurori da nufin fadada ayyukan jin kai a Gaza tare da yin kira da a tsagaita wuta a fadan ba tare da bata lokaci ba don ayyukan jin kai.
A yanzu haka dai ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Amurka, Masar, Isra’ila da Qatar don neman a dakatar da yakin a kuma sako mutanen da mayakan Hamas su ka yi garkuwa da su.
Yakin na Gaza ya fara ne a lokacin da mayakan kungiyar Hamas suka kai wa Isra’ila hari a ranar 7 ga watan Oktoba, inda suka kashe mutane 1,200 tare da yin garkuwa da mutane 253, bisa ga kididdigar Isra’ila. A wani mataki na ramuwar gayya, Isra’ila ta kaddamar da farmakin soji a Gaza wanda hukumomin lafiya suka ce ya yi sanadin kisan Falasdinawa sama da 28,000 yayin da ake fargabar wasu dubban gawarwaki sun makale a baraguzan gine-gine.
Kuri’ar da ta yiwu majalisar ta kada na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke shirin kai hari a yankin Rafah da ke kudancin Gaza, inda Falasdinawa sama da miliyan daya suka nemi mafaka, lamarin da ya sa ƙasashen duniya suka nuna damuwa kan cewa irin wannan matakin zai ƙara tsananta matsalar jin kai a Gaza.