Majalisa ta dakatar da sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku

1
146

Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Abdul Ningi na tsawon watanni uku kan zargin cewa an yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a Kasafin Kuɗin bana.

Neptune Hausa ta ruwaito cewa hatsaniya ta soma kaurewa a zauren Majalisar Dattawan, yayin da sanatoci ke muhawara kan zargin cushe a cikin kasafin kuɗin ƙasar wanda shugaban ƙungiyar Sanatocin Arewa, Abdul Ningi ya yi a wata tattaunawa da sashen Hausa na BBC.

Tun da farko shugaban kwamitin Kasafin Kuɗi na majalisar, Sanata Olamilekan Adeola daga jihar Ogun ya gabatar da ƙorafi kan tattaunawar da Sanata Ningi ya yi da manema labaran.

KU KUMA KARANTA: Hatsaniya ta ɓarke a Majalisar Dattawa kan kuɗin rabon tallafi

Ya soki lamirin kalaman Sanata Ningi wanda ke wakiltar Bauchi ta Tsakiya kan cewa ana amfani da Kasafin Kuɗi iri biyu a ƙasar.

Tun kafin hukuncin da majalisar ta ɗauka, Sanata Ningi wanda ya yi ƙoƙarin kare kansa, ya ce ba a fahimci kalaman nasa ba.

1 COMMENT

Leave a Reply