Majalisa ta amince da naira tiriliyan 1.28 kasafin kuɗin Abuja

0
142

A jiya Talata Majalisar Wakilai ta Najeriya ta amince da ƙudurin kasafin kuɗi na naira tiriliyan N1.28t na kasafin kuɗin babban birnin tarayya Abuja na 2024.

Majalisar ta amince da kasafin kuɗin ne bayan da shugaban kwamitin majalisa kan birnin tarayya, Mukhtar Betara ya gabatar da ƙudurin neman amincewa da kasafin kuɗin.

Yayin gabatar da ƙudurin, Betara ya ce, “Majalisar ta karɓi rahoton kwamitocin majalisar kan birnin tarayya da kuma na ƙananan hukomomin birnin tarayya, kan ƙudurin amincewa da dokar lalitar asusun birnin Abuja.”

KU KUMA KARANTA: Majalisun Dokokin Najeriya sun amince da naira tiriliyan 28.77 a matsayin kasafin kuɗin 2024

Adadin kuɗin da aka amince da shi shi ne, Naira tiriliyan ɗaya da biliyan ɗari biyu da tamanin da biyu, da miliyan ɗari biyu da saba’in, da dubu shida da goma, da ɗari biyu da tamanin da uku (N1,282,270,610,283).

Daga wannan jimilla, za a kashe Naira biliyan ɗari da arba’in N140.915 kan lamuran ma’aikata, sai Naira biliyan ɗari uku da saba’in da uku N373.027 na kuɗaɗen gudanarwa, sai kuma Naira biliyan ɗari bakwai da sittin da takwas N768.328 kan ayyukan raya-ƙasa a birnin na Abuja.

Tun da fari dai ministan babban birnin tarayyar, Nyeson Wike ya bayyana gaban kwamitin bai-ɗaya na birnin tarayya, da kuma na ƙananan hukumomin birnin tarayyar, inda ya kare batutuwa da alƙaluman kasafin kuɗin.

Leave a Reply