No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani mai wankin mota ya tsallake rijiya da baya lokacin da ya yi hatsari da matar lokacin da ya gwada tuƙata a unguwar Rumueme da ke Fatakwal a jihar Ribas.

Mai amfani da Facebook, Justice Ori wanda ya wallafa hotuna daga wurin ya ce lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, 29 ga Oktoba, 2023.

“Ya faru da yammacin yau a unguwar Rumueme da ke Fatakwal. Wani mutum ya tuƙa motarsa ​​ya nufi wajen wankin mota, mai wankin mota bayan ya wanke motar ya yanke shawarar gwada ƙwarewarsa ta hanyar tuƙa motar, abu na gaba da muka gani shi ne motar ta tsunduma a cikin magudanar ruwa. 

Mutanen da ke kusa da wajen sun taimaka sun fitar ta daga magudanar ruwan, yayin da mai wankin motar ya tsira da ransa.  Motar ta ci karo, ta karce, yayin da mai motar bai san faruwar lamarin ba har zuwa lokacin da aka buga wannan labari,” ya rubuta.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...