Shugaban ƙungiyar maharba a jihar, Ɗantala Adamu, ya shaida wa Aminiya cewa sun kama mutunen huɗu a wani tsauni da ke kan iyakar ƙananan Hukumomin Bali da Arɗo-Kola a daren Juma’a.
Ya ce waɗanda suka kama ɗin na cikin gungun ‘yan ta’addan da suke sace jama’a a ƙauyuka da ke ƙananan Hukumomin.
Ya ce waɗanda suka kama sun bayyana cewa suna da hannu a cikin ayyukan ta’addanci tare da sace mutane .
Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama mai suna Kwamanda, ya shaida wa wakilinmu cewa shi ne shugaba a cikin dabar masu sace mutane kuma yana da yara shida waɗanda yake amfani da su wajen sace mutanen.
KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga sun kashe limami sun sace uwa da ’ya’yanta a Kaduna
Kwamanda ya ce shi ɗan asalin ƙaramar Hukumar Ningi ne da ke Jihar Bauchi, kuma ya sace mutane da dama sannan ya karɓi miliyoyin kuɗaɗe daga hannun ‘yan uwansu.
Ya ce wani mutum daga anguwan Baba Yau a cikin garin Jalingo, babban birnin jihar, wanda ya ce shi ne yake kawo masu bindigogi da albarusai.
Maharban dai sun miƙa waɗanda suka kama a fadar Sarkin Jalingo domin kafa shaida kafin a miƙa su ga jami’an ‘yan sanda