Wani mahaifi mai shekara 42 mai suna Babatunde Afolayan, ya faɗa komar jami’an ’yan sanda a Jihar Legas, bisa zarginsa da shafe tsawon shekara uku yana yi wa ’yar cikinsa fyaɗe.
Aminiya ta rawaito cewa mutumin, wanda mazaunin unguwar Ikorodu ne da ke Jihar ta Legas, ya riƙa yi wa ɗiyar tasa fyaɗe tun tana shekara 10 a duniya.
Asirin mutumin ya fara tonuwa ne a lokacin da malaman makarantar da ‘yar tasa take zuwa suka fahimci tana wasu sababbin ɗabi’u, wanda hakan ya sa suka miƙa ta wajen limamin makarantar domin ya ba ta shawarwari.
Bayanai sun nuna a yayin ɗaya daga cikin irin waɗannan zaman na ba da shawara ne yarinyar ta bayyana wa limamin cewa mahifin nata ya shafe tsawon shekara uku yana lalata da ita.
Wata majiya a makarantar da ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da hurumin yin magana ta ce ce, “An fara gano bakin zaren ne a lokacin da aka ga yarinyar ta fara nuna wasu bakin halaye da ba kasafai ake ganin yara da su ba, kuma babu wanda ya san me ya kamata a yi a kai.
KU KUMA KARANTA: Matashi ya yi wa ’yar shekara 62 fyaɗe a Borno
“Haka ne ya sa aka kai ƙorafin ga shugaban makarantar, wanda shi kuma ya yanke shawararcewa za a tura ta wajen limamin makarantar domin ya ba ta shawara.”
Bayan haka ne sai shugaban makarantar ya kai ƙorafin ga wani ofishin ’yan sanda da ke kusa da makarantar, wanda hakan ya kai ga kama mahaifin yarinyar, yayin da ita kuma aka garzaya da ita asibiti domin a duba lafiyarta.
Da wakilinmu ya tuntuɓi Kakakin Rundunar ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce, “Yanzu haka wanda ake zargin yana hannunmu, ita kuma yarinyar an garzaya da ita asibiti ana duba lafiyarta. Yanzu haka kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin,” i ji shi.