Daga Idris Umar, Zariya
Shugaba cibiyar aikin gona ta jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya Farfesa Ado Yusuf, ya ƙaryata jita-jitan da ake yaɗawa akan amfani da (GMO) Genetically Modified Oganisms Element wajan binciken samar da sinadaran kare kai daga miyagun cutuka da ka iya maka amfanin Gona a ɓangaren aikin gona da makamantansu
KU KUMA KARANTA:Gwamnan Kano ya ƙaddamar da ayyukan gadar gadojin sama a jihar
Shugaban ya ƙaryata zargezargen ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan addamar da taron karawa juna sani da cibiyar ta shirya wanda suka kira shi da (Annual Research Review and Planing Meeting North West Zonal Refils Workshop) taron ya gudana ne a bubban ɗakin taro na Balarabe Tanimu Conference Hall dake harabar ma’aikatar.