Mafi ƙarancin sadaki a Najeriya ya koma kusan naira 100,000

Kwamitin ganin wata na mai alfarma sarkin musulmin Najeriya ya ce mafi ƙarancin kuɗin sadaki a ƙasar ya koma 99,241.

Cikin wata sanarwar da kwamitin ke wallafawa a kowace rana a shafukansa na sada zumunta ya nuna cewa a yanzu mafi ƙarancin kuɗin sadakin shi ne 99,241.

Ƙaruwar kuɗin sadakin ba ya rasa nasaba da faɗuwar darajar kuɗin Najeriya, wani abu da ke ƙara jefa tattalin arzikin ƙasar cikin mummunan hali.

KU KUMA KARANTA: Waliyin amarya ya sace sadaki ana tsaka da ɗaurin aure a Kano

Shi dai kuɗin sadaki ana lissafa shi da darajar zinare da azurfa a kasuwannin duniya.

A watan da ya gabata mafi ƙarancin sadaki a ƙasar bai haura naira 70,000 ba.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *