A karshe Majalisar Dattawa ta fitar da bayanan kuɗaɗen da aka ware wa ma’aikatu da sauran ɓangarori a kasafin shekarar 2024 da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar.
A ranar Laraba Tinubu ya gabatar da kasafin na naira tiriliyan 27.5, ba tare da bayanin kason da ware wa ma’aikatu da ɓangarori ba, lamarin da ya sa ’yan Najeriya guna-guni.
Sanatoci sun nuna damuwa kan rashin samun ƙarin bayanin kasafin, inda suka buƙaci a dakatar da nazarinsa har sai an kawo bayanan.
Sai dai duk da haka Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu a kan kasafin, washegari da dare Kwamitin Kasafi ya fitar da bayanin abin da ma’aikatu da bangarorin za su samu.
KU KUMA KARANTA: Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024
Ga jerin ma’aikatun da suka samu kaso mafi tsoka:
Ma’aikatar Tsaro: Naira biliyan 308.2
Ma’aikatar Ayyuka: Naira biliyan 521.3
Ma’aikatar Kuɗaɗe: biliyan N519.9
Ma’aikatar Lafiya: Biliyan N304.4
Ma’ikatar Ilimi: Biliyan N265.4
Ma’aikatar Wutar Lantarki: Biliyan N264.2
Kamfanoin Gwamnati: Biliyan N820.9
Ausun Manyan Makarantu (TETFund): Biliyan N665
Ma’aikatar Gidaje: Biliyan N96.9
Ma’aiatar Ruwa: Biliyan 87.7
Ma’aikatar ’Yan Sanda: Biliyan N69.
Majalisar Dokoki: Biliyan 198
Ma’aikatar Neja Delta: Biliyan 324.8
Hukumar UBEC: Biliya 251.4
Hukumar Shari’a: Biliyan 165
Hukumar Arewa maso Gabas: Biliya 126
Asusun Kula da Lfiya a matakin farko: Biliyan 125.7.