Ma’aikatun da suka fi samun kuɗi a kasafin 2024

0
196

A karshe Majalisar Dattawa ta fitar da bayanan kuɗaɗen da aka ware wa ma’aikatu da sauran ɓangarori a kasafin shekarar 2024 da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar.

A ranar Laraba Tinubu ya gabatar da kasafin na naira tiriliyan 27.5, ba tare da bayanin kason da ware wa ma’aikatu da ɓangarori ba, lamarin da ya sa ’yan Najeriya guna-guni.

Sanatoci sun nuna damuwa kan rashin samun ƙarin bayanin kasafin, inda suka buƙaci a dakatar da nazarinsa har sai an kawo bayanan.

Sai dai duk da haka Majalisar Dattawa ta kammala karatu na biyu a kan kasafin, washegari da dare Kwamitin Kasafi ya fitar da bayanin abin da ma’aikatu da bangarorin za su samu.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin 2024

Ga jerin ma’aikatun da suka samu kaso mafi tsoka:

Ma’aikatar Tsaro: Naira biliyan 308.2

Ma’aikatar Ayyuka: Naira biliyan 521.3

Ma’aikatar Kuɗaɗe: biliyan N519.9

Ma’aikatar Lafiya: Biliyan N304.4

Ma’ikatar Ilimi: Biliyan N265.4

Ma’aikatar Wutar Lantarki: Biliyan N264.2

Kamfanoin Gwamnati: Biliyan N820.9

Ausun Manyan Makarantu (TETFund): Biliyan N665

Ma’aikatar Gidaje: Biliyan N96.9

Ma’aiatar Ruwa: Biliyan 87.7

Ma’aikatar ’Yan Sanda: Biliyan N69.

Majalisar Dokoki: Biliyan 198

Ma’aikatar Neja Delta: Biliyan 324.8

Hukumar UBEC: Biliya 251.4

Hukumar Shari’a: Biliyan 165

Hukumar Arewa maso Gabas: Biliya 126

Asusun Kula da Lfiya a matakin farko: Biliyan 125.7.

Leave a Reply