Ma’aikatan EU sun yi zanga-zanga kan adawa da yaƙin Isra’ila a Gaza

0
69

Sama da ma’aikatan cibiyoyin Tarayyar Turai 100 ne suka hallara a Brussels a wata zanga-zangar adawa da yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Masu zanga-zangar sun ajiye fararen ƙyallaye uku masu nuna alamar likkafani da jini a jikinsu a dandalin da ke wajen babban ofishin hukumar Tarayyar Turai da ke babban birnin Belgium.

A jikin ƙyallayen an rubuta kalmomin dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar EU da yarjejeniyar kisan kare dangi, a wani mataki na nuna rashin amincewa da yadda Isra’ila ta mayar da martani ga hare-haren da kungiyoyin gwagwarmaya karkashin jagorancin Hamas suka kai a ranar 7 ga Oktoba.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah wadai da harin Isra’ila a Rafah

Wani ma’aikacin Hukumar Tarayyar Turai Manus Carlisle ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa “Muna wani taro na lumana, domin tsayawa tsayin daka wajen kare hakki da ka’idoji da ƙimar da cibiyoyin Turai suka ginu akai.”

Leave a Reply