Ma mallakin shafin Facebook ya cire shafin mawaƙi Rarara
Rahotannin sun bayyana cewa mabiya Dauda Kahutu Rarara a shafin sada zumunta na Facebook da yawa sun tura saƙonnin neman a cire shafin mawaƙin daga dandalin, saboda wata waƙar yabo da ya yi wa gwamnatin Najeriya kwanan nan.
Ga dukkan alamu kamfanin sada zumunta na Meta wanda aka fi sani da Facebook ya cire shafin fitaccen mawaƙin nan ɗan arewacin Najeriya mai suna Dauda Kahutu Rarara daga dandalin, bayan da mabiyan mawaƙin suka kai wa kamfanin ƙorafi.
Matakin cire shafin dai na zuwa ne bayan da Rarara ya wallafa wata waƙa ta yabon shugaban Najeriya Bola Tinubu saboda yadda yake magance matsalolin talauci da tsaro a Najeriya.
KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga sun sako mahaifiyar Rarara
A ranar Asabar ne dai aka cire shafin sada zumuntar mawaƙin na Facebook, wanda ke da mabiya sama da miliyan ɗaya. Waƙar da mawaƙin ya yi ta yaba wa Tinubu kan yadda ya ke kawar da yunwa da rashin tsaro a Arewacin ƙasar, a cewarsa “yanzu ‘yan Arewa sun yi bankwana da yunwa, rashin tsaro, da talauci.”
Waƙar, wadda ta janyo cece-ku-ce dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zanga-zangar gama-gari daga ranar ɗaya ga watan Agusta, sakamakon tashin farashin abinci da kuma taɓarɓarewar tattalin arziƙi a ƙasar da ta fi yawan jama’a a nahiyar Afrika.
Duk da yabon da Rarara ya ke wa gwamnatin, a kwanan nan sai da mahaifiyarsa ta yi kwanaki uku a hannun ‘yan bindiga, kafin daga baya suka sako ta.