MƊD na neman kuɗaɗe don magance matsalar ‘yan gudun hijira a duniya

0
138

Wasu alƙaluma da ake da su na bayyana cewa duk  da girman rikicin Gaza, bai kamata ƙasashen duniya su manta da dubun-dubatar ‘yan gudun hijira a duniya ba, kalaman Shugaban hukumar ‘yan gudun hijira, Filippo Grandi, a wajen buɗe taron kolin ‘yan gudun hijira na duniya, wanda ke gudana har zuwa ranar 15 ga watan Disamba na wannan shekara  a Geneva.

Shugaban hukumar ‘yan gudun hijira, Filippo Grandi ya bayyana damuwa matuƙa,” ,ya kuma bayyana cewa, ya zama wajibi hukumar ta sallami kusan mukamai 900 daga cikin 20,000.

Ya zuwa wannan lokaci ƙungiyar ta na buƙatar dala miliyan 400 kusan (Euro miliyan 371) nan da ƙarshen shekara.

Yaƙi a Ukraine, tashe-tashen hankula a Sudan, Habasha, rikicin jin kai a Afghanistan,hukumar ta fitar da wasu alƙaluma inda ta ke cewa sama da mutane miliyan 114 ne suka rasa matsugunansu a faɗin duniya a ƙarshen watan Satumba.

KU KUMA KARANTA: Australia ta goyi bayan ƙudurin MƊD na tsagaita wuta a Gaza

Rahoto daga Hukumar na nuni yawan ‘yan gudun hijira a duniya ya ninka a cikin shekaru bakwai da suka gabata, inda ya kai mutane miliyan 36.4 a tsakiyar shekarar 2023.

Shugaban hukumar ya tabbatar da cewa “babban bala’in bil’adama na faruwa a zirin Gaza”, kuma ya yi hasashen “ƙarin mutuwa da wahala a tsakanin fararen hula, da kuma ƙara yawan yan gudun hijirar daga yankin.

Ya sake yin nuni da cewa a ranar Laraba shirin gwamnatin Burtaniya na mai da hankali kan korar baƙin haure da suka isa Birtaniya ba bisa ƙa’ida ba zuwa ƙasar Rwanda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here