MƊD ta yi Allah wadai da harin Bama

0
338
MƊD ta yi Allah wadai da harin Bama

MƊD ta yi Allah wadai da harin Bama

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah-wadai da wani harin da ‘yan ta’adda suka kai a garin Darul Jamal, dake yankin Bama na Jihar Borno.

Mista Mohamed Malick Fall, Babban Jami’i mai Kula da Ayyukan Jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, ya bayyana matukar bakin cikinsa kan lamarin, wanda ya faru a yammacin ranar 5 ga watan Satumba.

“Ina matukar bakin ciki da rahoton kisan da aka yi wa sojoji da fararen hula da dama a ranar Juma’a a kauyen Darajamal da ke karamar hukumar Bama (LGA), a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya,” inji Fall.

“Bai kamata fararen hula su zama abin hari ba”.

Rahotannin farko sun nuna cewa an kashe fararen hula fiye da 50, inda ake zargin an yi garkuwa da wadanda ba a san adadinsu ba. Wasu da dama sun gudu, kuma gidaje fiye da 20 sun ƙone ƙurmus a lokacin harin. Adadin wadanda suka jikkata na iya karuwa yayin da ake samun karin bayanai.

A madadin Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Fall ya mika ta’aziyya ga iyalan wadanda kai harin ya shafa, gwamnati, da kuma al’ummar jihar Borno, tare da yi wa wadanda suka ji rauni fatan samun sauki cikin gaggawa.

KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro a Neja sun gano bama-bamai da aka binne

“Ina ƙira ga hukumomin tsaro da su kamo wadanda suka kai wannan danyen aikin. Ina kuma kira da a gaggauta sakin duk wadanda aka sace,” inji shi.

Jami’in Majalisar Ɗinkin Duniya ya bayyana lamarin a matsayin wani mummunan tunatarwa kan yadda tashe-tashen hankula da rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a jihar Borno a duk shekara.

Rahotanni sun nuna cewa an dade ana kashe fararen hula, yan gudun hijira (IDP), manoma, matafiya, da ‘yan kasuwa a irin wadannan hare-haren. Dabarun da Yan ta’adda ke amfani da su sun hada da bama-bamai, da kai harin ƙunar baƙin wake, da dai sauran munanan hanyoyi.

Bugu da ƙari, Fall ya lura cewa jihohin Adamawa da Yobe da ke makwabtaka da jihar Borno ba su tsira ba, inda aka kai hare-hare a cibiyoyin kiwon lafiya, da kuma kasuwanni.

“Ina ƙira ga ɓangarorin da ke rikici da su kare fararen hula da dukiyoyinsu da kuma bin dokokin ayyukan jin kai na duniya
da kare hakkin dan Adam,” in ji shi.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta sake jaddada aniyar ta na ci gaba da tallafawa wadanda rikici ya shafa a Najeriya, a kokarin da gwamnatin ke yi na kara mayar da martanni.

Leave a Reply