Likitoci a Zamfara sun dakatar da shiga yajin aiki

1
185

Likitoci a asibitin ƙwararru na Yariman Bakura, AYBSH, Gusau a Zamfara sun dakatar da shirinsu na shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar 4 ga watan Satumba.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar likitocin Najeriya reshen jihar NMA ta fitar a ranar Juma’a mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na jiha, Dakta Sanusi Bello da sakataren ƙungiyar, Dakta Murtala Shinkafi.

Idan ba a manta ba, Neptune Hausa ta kawo labarin cewa likitocin sun sanya ranar 4 ga watan Satumba za su fara yajin aikin sai baba-ta-gani kan rashin biyansu albashi da alawus-alawus da gwamnatin jihar ta yi.

“Wannan shi ne don sanar da jama’a cewa an dakatar da yajin aikin masana’antu da likitocin AYBSH suka shirya.”

Likitocin sun bayyana cewa gwamnatin jihar ta warware rikicin masana’antu cikin ruwan sanyi wanda hukumar NMA ta jihar ta gamsu. Sanarwar ta ce “Dukkan albashin likitocin da abin ya shafa an daidaita su,” in ji sanarwar.

KU KUMA KARANTA: NLC ta ayyana yajin aikin gargaɗi na kwana biyu kan cire tallafin mai

Sun ƙara da cewa, shirye-shirye sun kai ga cimma matsaya kan kuɗaɗen alawus-alawus na masu ba da shawara da na Farfesoshi, da kuma batun cire wasu kamfanoni.

Sun yaba da tsoma bakin Gwamna Dauda Lawal, Sakataren Gwamnatin Jiha, Abubakar Nakwada, Sarkin Gusau, Ibrahim Bello, ‘Nigerian Labour Congress’ da kuma kafafen yaɗa labarai, wajen warware batutuwan da ake taƙaddama a kai.

1 COMMENT

Leave a Reply