Lawan ya musanta sha’awar shugabancin sake zama shugaban majalisar dattawa

0
938

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya musanta rahotannin da kafafen yaɗa labarai suka yaɗa cewa ya shiga takarar neman shugabancin majalisar wakilai ta 10.

Lawan ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata.

“Na karanta wasu rahotannin kafafen yaɗa labarai cewa na shiga takarar neman shugabancin majalisar dattawa ta 10.

“A ƙa’ida da ban mayar da martani ga waɗannan rahotanni ba amma idan ba a ƙaryata ba, suna da ɗabi’ar haifar da ruɗani na gaskiya.

KU KUMA KARANTA: Shugabancin majalisar wakilai: Ya kamata mutunta martabar jam’iyya – Anamero Dakeri

“Gaskiyar magana ita ce ban taɓa faɗawa kowa ko ganawa da kowa cewa ni zan tsaya takarar shugabancin majalisar dattawa ta 10 ba, don haka jama’a su yi watsi da waɗannan rahotannin.

“Gaskiyar lamarin dai ina cikin jagorancin babbar jam’iyyar mu ta APC, ina neman ganin an magance ɗimbin matsalolin da suka taso a fafatawar neman shugabancin majalisar wakilai ta 10, kuma zan ci gaba da mai da hankali kan hakan.

Leave a Reply