No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani mutum mai shekaru 39 da haihuwa da aka kama da laifin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 7 a jihar Adamawa ya ɗora laifin da ya aikata a kan giyar Burukutu da ya sha.

 Wanda ake zargin, Sadiq Ahmed, da ke kan titin Abuja a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a jihar ya amsa laifin lalata ƙaramar yarinya a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, 2023.

Yayin da ake yi masa tambayoyi a hedikwatar ‘yan sanda a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, wanda ake zargin ya ce ya aikata laifin ne a lokacin da ya bugu da Burukutu.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Okada ya yiwa mace mai ciki fyaɗe a Benuwe

Ya ce bai ɗauki komai ba sai Burukutu kuma ya yi nadamar lalata yarinyar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan ƙorafin da mahaifin yarinya ya kai.

Mahaifin ya sanar da ‘yan sanda cewa wanda ake zargin ya zo gidan sa ne a lokacin da ba su nan ya ba ‘yar sa kuɗi naira 10 sannan ya lalata ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO) ta ce kwamishinan ‘yan sandan, Afolabi Babatola, wanda ya nuna damuwarsa kan lamarin, ya sha alwashin tabbatar da gurfanar da wanda ake zargin a gaban Kotu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...