Connect with us

Fyaɗe

Laifin giyar burkutu da na sha, cewar wanda ya yi wa ‘yar shekara bakwai fyaɗe

Published

on

Wani mutum mai shekaru 39 da haihuwa da aka kama da laifin lalata da wata yarinya ‘yar shekara 7 a jihar Adamawa ya ɗora laifin da ya aikata a kan giyar Burukutu da ya sha.

 Wanda ake zargin, Sadiq Ahmed, da ke kan titin Abuja a ƙaramar hukumar Yola ta Kudu a jihar ya amsa laifin lalata ƙaramar yarinya a ranar Litinin, 12 ga watan Yuni, 2023.

Yayin da ake yi masa tambayoyi a hedikwatar ‘yan sanda a ranar Talata, 13 ga watan Yuni, wanda ake zargin ya ce ya aikata laifin ne a lokacin da ya bugu da Burukutu.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Okada ya yiwa mace mai ciki fyaɗe a Benuwe

Ya ce bai ɗauki komai ba sai Burukutu kuma ya yi nadamar lalata yarinyar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan ƙorafin da mahaifin yarinya ya kai.

Mahaifin ya sanar da ‘yan sanda cewa wanda ake zargin ya zo gidan sa ne a lokacin da ba su nan ya ba ‘yar sa kuɗi naira 10 sannan ya lalata ta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO) ta ce kwamishinan ‘yan sandan, Afolabi Babatola, wanda ya nuna damuwarsa kan lamarin, ya sha alwashin tabbatar da gurfanar da wanda ake zargin a gaban Kotu.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Fyaɗe

Fyaɗe: An ba da belin Dani Alves, tsohon ɗan wasan Brazil kan dala miliyan 1.1

Published

on

Wata kotu a Sifaniya ta ba da belin tsohon ɗan ƙwallon ƙafar Brazil da kuma Barcelona, Dani Alves, kan dala miliyan 1.1.

Sauran sharuɗɗan belin sun haɗa da cewa Alves zai ajiye fasfo ɗinsa na Brazili da na Sifaniya, domin gudun ka da ya fice daga Sifaniyar.

A ranar Laraba ne wata kotun Barcelona ta ce za a iya sakin Dani Alves daga gidan yari kan belin dala miliyan 1.1, yayin da yake aukaka ara kan shari’ar da ake masa kan aikata fyaɗe, bayan ya yi zaman kusan kwatan wa’adin shekaru huɗu na hukunci.

Haka nan kuma, kotun ta ɗora masa dokar hana Alves zuwa kusa da wadda ya aikata laifin kanta, da tazarar mita 1,000.

KU KUMA KARANTA: Ana yi wa yara fyaɗe sakamakon yaƙin da ke faruwa a Sudan – MƊD

An tsare tsohon ɗan wasan baya na Barcelona da Juventus da PSG a wani gidan yari na Barcelona tun watan Janairun 2023.

An yanke wa Alves hukunci ranar 22 ga Fabrairu, kan laifin yi wata mata fyaɗe a banɗaki wani gidan rawa na Barcelona a 2022, kuma aka umarce shi ya biya ta Euro dubu 150,000.

Sai dai ya ɗaukaka ƙara kan hukunci, kasancewar hukuncin ba shi ne na ƙarshe ba.

Continue Reading

Fyaɗe

Wani hedimasta ya yi wa ‘yar shekara shida fyaɗe

Published

on

An kama wani hedimasta a jihar Bauchi da laifin yi wa ‘yar shekara 6 fyaɗe.

Mai shari’a Nana Fatimah Jibrin, shugabar babbar kotun jihar Bauchi mai lamba 11, ta yanke hukuncin ɗaurin shekaru 11 a gidan kaso ga wani Hedimasta a garin Burra da ke ƙaramar hukumar Ningi mai suna Jalaludeen Zakari bisa samunsa da laifin yin lalata da wata yarinya yar shekara 6.

Yarinyar ta kasance a makarantar don yin jarabawar shiga makarantar amma Zakari ya tsare ta tsawon sa’o’i bayan an rufe makarantar a hukumance.

Barista Dayabu Ayuba, lauya mai shigar da ƙara kuma lauyan jiha a ma’aikatar shari’a ta jihar Bauchi, wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Talata, 2 ga watan Janairu, 2023, ya ce wanda ake tuhumar ya shigar da yatsarsa a cikin al’aurar yarinyar.

KU KUMA KARANTA: Shekara 3 bayan ya yi wa ‘yar shekara 4 fyaɗe, kotu ta yanke mishi hukunci

Ayuba ya ce a lokacin da ake shari’ar, shaidu uku ciki har da wanda aka yi wa lalata, sun ba da shaida a gaban kotun.

“Mai laifin ya buƙaci yarinyar da ta tsaya, ya sallami sauran ɗaliban bayan an tashi daga makaranta, ba tare da bayar da dalilin tsawaita zaman yarinyar ba. 

Yayin da aka bar ta a baya, hedimasta ya ya kai mata harin lalata, wanda ya yi daidai da fyaɗe a shari’ance,” inji shi.

Ayuba ya ce an yanke hukuncin ne a watan Yulin wannan shekara bayan Jalaludeen ya roƙi kotu da ta yi masa sassauci.

Continue Reading

Fyaɗe

Kotu a Kebbi ta ɗaure yaron da ya yi wa ƙananan yara biyu fyaɗe

Published

on

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Birnin kebbi ta samu wani matashi ɗan shekara 16 Habibu Umar da laifin yin lalata da yara ƴan mata kuma aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan gyaran hali.

Ɗan sanda mai gabatar da ƙara Insp.  Muntari Mati, a ranar Alhamis, 23 ga watan Nuwamba, 2023, a wata ƙara mai lamba BK/538C/223,  ya gabatar da Habibu Umar a gaban kotu bisa tuhuma guda ɗaya na cin zarafi ta lalata wanda ya saɓawa sashe na 263 na ƙundin laifuffukan Penal na jihar Kebbi.

Habibu ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi a gaban kotu, Alkalin Kotun Samaila Kakale Mungadi don haka ya yanke wa Habibu hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari tare da zaɓin biyan tarar naira dubu ɗari da hamsin (N150,000).

KU KUMA KARANTA: An kama yaro ɗan shekara 16 a Kebbi bayan ya yi wa ƙananan yara 2 fyaɗe

Zaku iya tuna cewa Neptune Hausa ta ruwaito cewa jami’an tsaron Masarautar Gwandu ne suka kama Habibu Umar wanda hakan ya sa aka ƙara ɗaukar mataki.

Bayan an yi masa tambayoyi na farko a Fadar Ubandoman Gwandu, daga baya aka miƙa shi ga hukumar Hisbah ta jihar Kebbi, bayan da aka yi zargin ya lalata wasu ƙananan ‘yan mata biyu masu shekaru biyar da shida a wani daji da ke tsakanin unguwar Badariya da Barikin Sojoji a Birnin kebbi a ranar 21 ga Nuwamba 2023.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like