Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama haramtattun nakiyoyi 6,240 a hanyar Yauri zuwa Jega da ke Jihar Kebbi.
Kwanturolan Kwastam na Jihar Kebbi, Iheanacho Ernest Ojike, ya ce hukumar ta damka wa hukumar tsaro ta DSS wadannan nakiyoyi da aka kama.
Kwanturola Iheanacho Ernest Ojike, ya bayyana cewa an kama nakiyoyin ne a cikin wasu kwalaye 40 da kuma buhuna, kuma masu hatsari ne.
KU KUMA KARANTA: DSS ta sako wacce ta soki gwamnatin Kaduna a Facebook
Iheanacho Ojike ya ce an kama wasu mutum biyu da ke da alaka da makaman kuma an gurfanar da su a gaban kuliya, inda alkali ya ba da umarnin tsare su.
A cewarsa, jami’an tsaron hadin gwiwar kwastam, sojoji, ’yan sanda, DSS da kuma hukumar shige da fice ne suka kama mamakan, bayan samun bayanan sirri.