Kwankwaso ya caccaki ‘yansanda kan yunƙurin hana mauludin Tijjaniyya a Kano

0
238
Kwankwaso ya caccaki 'yansanda kan yunƙurin hana mauludin Tijjaniyya a Kano

Kwankwaso ya caccaki ‘yansanda kan yunƙurin hana mauludin Tijjaniyya a Kano

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya Darikar Tijjaniyya murnar kammala taron Mauludin Sheikh Ibrahim Inyass da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha a jihar Kano, inda ya ce an gudanar da mauludin cikin nasara.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X , Kwankwaso ya mika sakon taya murna ga manyan shugabanni masu ruwa da tsaki, ciki har da Mai Martaba Khalifa Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano, da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, kan shirya wannan babbar taro mai tarihi.

KU KUMA KARANTA:Zaɓen 2027: Ba mu cimma yarjejeniyar haɗewa da PDP, NNPP ba – Peter Obi

Sai dai, Kwankwaso ya nuna damuwarsa kan wani “gargadin kai harin ta’addanci” da rundunar ‘yansandan jihar Kano ta fitar a daren gabanin taron, inda ya soki wannan gargadi, yana mai cewa bai dace ba, kuma yana iya yin barazana ga nasarar taron tare da jefa tsoro a zukatan mazauna jihar da baki daga kasashen waje.

“Wannan hali na ‘yan sanda ba kawai ya jefa rayukan mutane a Kano cikin hadari ba, har ma ya bata sunan rundunar ‘yan sandan Najeriya a idon duniya, musamman ganin muhimmancin taron Mauludi a matakin kasa da kasa,” in ji shi.

Kwankwaso ya nuna cewa irin wadannan gargadin na ƙarya za su iya sanya mutane yin sakaci idan wata barazana ta gaskiya ta taso a nan gaba. Haka nan ya zargi ‘yan sanda da nuna bangaranci tare da alakanta ayyukansu da wani shirin gwamnatin tarayya na tsoma baki a harkokin jihar Kano

Leave a Reply