Kwankwaso ya ɗauki nauyin yin magani ga yaron da ke fama da ciwon yunwa a Katsina
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ɗauki nauyin jinyar wani yaro mai suna Abubakar Ibrahim, ɗan shekara 13 da ke fama da cutar tamowa.
Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa yaron dai mazaunin unguwar Yammawa ne, wani yanki a cikin birnin Katsina.
Bidiyon yaron ta karaɗe shafukan sada zumunta, inda ya nuna yadda ya ke fama da ciwon tasowa kuma ya ke neman taimako.
Daga nan ne sai shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Katsina, Armaya’u Abdulkadir, ya ce Kwankwaso ya ga bidiyon, kuma ya nuna damuwa kan halin da Ibrahim ke ciki.
A cewar Abdulkadir, Kwankwaso ya nuna niyyar daukar nauyin jinyar yaron a ziyarar ta’aziyyar da ya kai ga iyalan Yar’adua bisa rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasar.
Ya kara da cewa “Kwankwaso ya bada umarnin a kai Ibrahim Kano domin samun kulawar da ta dace da sauran kulawar da ake bukata.
KU KUMA KARANTA:Ni zan lashe zaɓen 2027 – Sanata Rabi’u Kwankwaso
“Nan da nan aka kai yaron asibitin Abdullahi Wase da ke unguwar Nasarawa a Kano, inda ya samu isassun magunguna
da hankali da kuma samar da abinci da ake bukata da sauran sinadaran gina jiki.
“Na gode wa Allah Madaukakin Sarki Ibrahim ya samu sauki, kuma an dawo da shi gida. Kamar yadda kake gani a yanzu, ya yi kyau kuma ya samu kumari. ”
Iyayen yaron da sauran al’ummar unguwar sun godewa Kwankwaso bisa wannan taimako da ya yi.