A ranar Laraba ne Ƙungiyar ‘yan jarida a Najeriya (NUJ) reshen jihar Zamfara, ta tabbatar da kisan ɗaya daga cikin mambobinta Alhaji Hamisu Danjibga, wakilin Muryar Najeriya (VON) a jihar.
Wata sanarwa da sakataren ƙungiyar NUJ na jihar, Ibrahim Ahmad ya fitar a Gusau, ya ce waɗanda suka kashe shi ne suka jefar da gawar marigayin a cikin sokaway.
“An gano gawar tasa ne sakamakon wani wari mara daɗi da yaran makarantar Islamiyya suka ji a bayan gidansa da yammacin Laraba 20 ga Satumba, 2023.
“Bayan fasa shaddar sokaway, an tabbatar da gawar Ɗanjibga ta danginsa da wasu maƙwabta,” in ji sanarwar.
KU KUMA KARANTA: Bayan biyan miliyan biyar, ‘yan bindiga sun saki ɗaya daga cikin masu yiwa ƙasa hidima da aka yi garkuwa da su a Zamfara
Wannan jarida ta tattaro cewa Ɗanjibga ya ɓata kwana uku kafin a gano gawarsa.
Majiyoyi sun ce da farko an tuntuɓi iyalan ne don su biya Naira miliyan ɗaya domin a sake shi, amma kafin a kai ga ƙididdige shi, wasu marasa fuska da ake zargin sun yi garkuwa da shi ne suka kashe shi.
Ita ma jaridar ta tattaro cewa ‘yan sanda sun kama mutum ɗaya da ake zargin yana da hannu wajen kashe ɗan jaridan.
Ƙungiyar ta NUJ ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalan mamacin, VON, da ɗaukacin al’ummar Zamfara.
Ta buƙaci hukumomin tsaro da su binciki lamarin sosai tare da gurfanar da waɗanda suka aikata wannan aika-aika a gaban ƙuliya.
An yi jana’izar marigayin a Gusau kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
[…] KU KUMA KARANTA: Kwana uku da ɓatan ɗan jarida a Zamfara, an samu gawarsa a rami […]