No menu items!

Sample Page Title

Date:

Ministan Harkokin Waje na Turkiyya Hakan Fidan ya halarci tattaunawar da Kwamitin Tuntuɓa kan Gaza ya shirya a Saudiyya, a wani ɓangare na yunƙurin cim ma tsagaita wuta a Gaza.

Kwamitin Tuntuɓa kan Gaza wanda mambobin Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta OIC suka kafa tare da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, sun haɗu don tattauna matakan haɓaka zamowar Falasɗinu ƙasa mai ‘yanci, da ƙara matsin lamba kan Isra’ila da ƙawayenta.

Majiyoyin diflomasiyya sun ce taron, wanda aka yi a babban birnin Saudiyya na Riyadh ya kawo ƙarshe, inda wakilai suka tattauna matakan da za su ɗauka yayin taron ƙoli na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi na OIC mai zuwa, wanda za a yi a birnin Banjul na Gambiya, ranar 4 ga Mayu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan Houthi na Yaman sun kai hari kan jiragen ruwan Isra’ila da Amurka da Birtaniya 102 a rikicin Gaza

Minista Fidan zai ci gaba da tattaunawarsa da ƙasashen duniya a Riyadh har zuwa Litinin, a cewar majiyar.

An shirya Fidan zai gana da takwaransa na Jordan, Ayman Safadi, da na Norway, Espen Barth Eide, da na Yemen, Shai Muhsin Zindani, da kuma jagoran manufofin ƙasashen waje na Tarayyar Turai, Joseph Borrell.

An kafa Kwamitin Tuntuɓa kan Gaza lokacin wani taron ƙoli na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta OIC da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, a watan Nuwamba don kawo ƙarshen rikicin Gaza, da taimakawa cimma zaman lafiya mai ɗorewa.

Isra’ila tana ƙaddamar da ƙazamin yaƙin kan Gaza, tun bayan harin da ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas ta ƙaddamar ranar 7 ga Oktoban bara.

Hare-haren sojin Isra’ila, wanda ya kashe Falasɗinawa 34,000 tun lokacin, inda hakan ya mayar da yankin da ke zaman matsugunin mutane miliyan 2.3, ya koma kufai, kuma ya janyo mafi yawancin farar hula suna fuskantar yunwa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...