Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya zai sake kaɗa ƙuri’a kan tsagaita wuta nan-take a Gaza, bayan Rasha da China sun hau kujerar-na-ƙi kan wani ƙuduri da Amurka ta gabatar.
Kawunan mambobin kwamitin sun rabu game da yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza tun ranar 7 ga watan Oktoba na 2023 bayan ƙungiyar Hamas ta kai mata harin ba-zata, inda suka amince da daftari biyu kawai daga cikin takwas, dukansu kan kai kayan jinƙai yankin.
Amurka, wadda mamba ce ta dindindin a kwamitin, tana goyon bayan Isra’ila.