Kwamitin Tsaro na MƊD na buƙatar gyara – Ministan Harkokin Wajen Turkiyya

0
120

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya jaddada buƙatar yin garambawul ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya bayyana gazawarsa wajen tunkarar al’amuran duniya da suka haɗa da na Gaza.

A rana ta biyu ta taron Ministocin Harkokin Wajen kasashen G20 a Brazil, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya halarci taron sake fasalin tsarin mulki na duniya a yau Alhamis, inda ya bayyana muhimmancin cibiyoyi masu inganci da kuma ingantattun hanyoyin gudanar da mulki a duniya don magance tashe-tashen hankula na yankuna a cikin sabon tsarin duniya na yau.

Ya ce ya zama wajibi a fahimci buƙatar samun sauyin, kuma ya kamata a ba da fifiko wajen yin garambawul ga Kwamitin Tsaro, a cewar majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya.

Fidan ya ce Majalisar ta yi watsi da martabar tsarin MƊD baki ɗaya, kuma ana buƙatar “tsari mai inganci da tsarin dimokuraɗiyya” bisa ƙa’idojin dokokin ƙasa da ƙasa.

Majiyoyin sun ce Fidan ya kuma lura cewa ya kamata tsarin hada-hadar kudi na ƙasa da ƙasa ya kasance “mai haɗo kowa da kowa bisa gaskiya da ƙa’ida kuma mai ɗorewa.”

Ya ce ya kamata cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa da bankunan ci gaban ƙasashe daban-daban su yi amfani da manufofin da suka dace da kasashe masu tasowa da wadanda ba su da ci gaba don cike giɓin da ke tsakanin ƙasashe masu tasowa.

KU KUMA KARANTA: Ministocin Tsaron Turkiyya da Djibouti sun sa hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa ta soji

Idan ba haka ba, in ji Fidan, ba za a iya cimma burin ci gaba mai ɗorewa ba.

Ya ƙara da cewa G20 na da muhimmiyar rawar da za ta taka wajen taimaka wa lamarin.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya kuma gana da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan Al Saud a yau Alhamis, inda suka tattauna kan halin da ake ciki a Gaza, a cewar majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya.

Ministocin sun yi musayar ra’ayi kan matakan da ƙasashen yankin za su iya ɗauka na tsagaita wuta na gaggawa a Gaza, da kuma samar da ƙasashe masu cin gashin kansu na Isra’ila da Falasɗinu, a cewar majiyoyin diflomasiyya.

“Fidan ya sanar da cewa taron Gaza da za a gudanar a taron diflomasiyya na Antalya mai zuwa zai zama “muhimmiyar dama.”

Bugu da ƙari, an tattauna dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu da tattalin arziki da haɗin gwiwa a fannin tsaron masana’antu, in ji majiyar.

Taron ya zo ne a gefen taron Ministocin Harkokin Wajen Ƙasashen G20 da ake yi a Brazil.

Leave a Reply