Kwamishinan ‘yan sandan Kwara ya ba da umarnin kama jami’in da ya bugu a cikin faifayin bidiyo

1
629

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Kwara, Paul Odama, ya bayar da umarnin kama wani sufeton ‘yan sanda mai suna Stephen Yohana a cikin wani faifayin bidiyo da aka nuno shi ya bugu.

Mista Yohana yana aiki ne a sashin Share, ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Okasanmi Ajayi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata cewa ɗan sandan da ya bugu a cikin wani faifayin bidiyo an gano shi Yohana ne.

“Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta cika da hoton bidiyon wani sifeton ‘yan sanda mai suna Stephen Yohana yana zagayawa a shafukan sada zumunta daban-daban cikin maye.

KU KUMA KARANTA: PSC ta amince da korar jami’an ‘yan sanda 3, ta kuma rage ma’aikata 5 daga aiki

“Bayan kallon faifayin bidiyon, kwamishinan ‘yan sanda, Paul Odama, ya ba da umarnin a gano ɗan sandan cikin gaggawa tare da kama shi.

“Rundunar tana so ta bayyana cewa sufeton ‘yan sandan da ke aiki da sashin Share a ƙaramar hukumar Irepodun ta jihar Kwara, an gano shi kuma a halin yanzu yana duba lafiyarsa a asibitin ‘yan sanda, domin sanin halin da ƙwaƙwalwarsa ke ciki.

“An lura cewa yadda aka nuno shi yana tamɓele, ya fi kama da rashin ƙwaƙwalwa, ba giya ba. “Sakamakon binciken lafiyarsa ne zai tabbatar da matakin da za a ɗauka na gaba a kansa.

“Saboda haka, kwamishinan ya ba da umarnin cewa babban mai kula da shi, jami’in ‘yan sanda na Rarraba ‘Divisional’ ya sanya wa sufeton kulawa sosai, har sai an kammala jinyarsa,” in ji ta.

1 COMMENT

Leave a Reply