Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Usaini Gumel, ya bayar da umarnin kamo wani Sufeto da aka zargi da nuna rashin ƙwarewa inda har kai ga hallaka wani mutum ɗaya tare da jikkata wasu mutane biyu a jihar.
Alfijir labarai ta rawaito sanarwa da SP Abdullahi Haruna Kiyawa mai magana da yawun rundunar ya fitar a ranar Laraba, ta ce rundunar ‘yan sanda na bin diddigin lamarin da ya faru a unguwar Kurna, ƙaramar hukumar Fagge jihar Kano a ranar 28 ga watan Nuwamba, 2023 inda wasu gungun matasa suka fafata da wani sifeton ‘yan sanda, wanda bai samu wani umurni daga rundunar ‘yan sandan ba ya harba bindigarsa, kuma abin takaicin shi ne ya raunata wasu mutane biyu tare da hallaka wani mutum guda .
Sanarwar ta ƙara da cewa, a halin yanzu kwamishinan ‘yan sanda, CP Mohammed Usaini Gumel, FIPMA, psc, ya umurci kwamandan yankin Dala, ACP Nuhu Mohammed Digi da ya kamo sufeton ‘yan sandan domin gudanar da bincike kan lamarin don ɗaukar matakan da suka dace akan shi.
KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ta ɓarke a Kano kan soke nasarar Abba Gida-Gida (Hotuna)
Sanarwar ta yi Allah wadai da abun da sufeton yan sandan ya gudanar, inda sanarwar tace kwamishinan yan sandan Kano ya himmatu tun da ya kama aiki a kano, don ganin ‘yan sanda suna gudanar da aikin su bisa ƙwarewa da sanin makamar aiki.
Kwamishanan ‘yan sandan ya miƙa ta’aziyyasa ga iyalan mamacin da addu’ar Allah ya jikansa, ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankulan su domin rundunar ta ɗauki lamarin da matukar muhimmanci tare da tabbatar da adalci da gaskiya.