Kwamishinan ‘yan sanda ya cire DPO da yaransa kan zaluntar jama’a

0
255

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Idowu Owohunwa, ya bayar da umarnin korar jami’in ‘yan sandan DPO na ofishin ‘yan sanda na Meiran da ke jihar Lagos bisa zargin karɓar kuɗi.

Tun da farko, wani Injiniya Ibrahim Saliu, wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai na PUNCH, ya yi iƙirarin cewa wasu ‘yan sandan da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Meiran a jihar Legas sun karɓo masa Naira 200,000 a ranar Asabar.

A cewar Saliu, jami’an tare da DPO sun yi barazanar ɗaure shi da ɗan uwansa idan har suka ka sa ba da takardar shaidar wayar da aka gani tare da ɗan uwan Saliu.

Ya ce, “DPO ya ɗauki wayoyin iPhone, ya cire takardar garanti, sannan ya bayyana cewa ni da ɗan uwana ɓarayi ne kuma ’yan fashi da makami ne.

Abu na gaba da na ji shi ne DPO ya ba su umarni a tsare mu kuma za a tsare mu da laifin sata da fashi da makami. mun yi mamaki.

KU KUMA KARANTA: Soludo ya rufe makaranta a Onitsha saboda zaluntar ɗaliba ‘yar shekara biyu

Saliu ya bayyana cewa an nemi ya biya su Naira 500,000 domin samun ‘yancinsu. Sun amince da Naira 200,000, wanda aka biya a tsabar kuɗi bisa ga umarnin jami’an.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter da ke tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa, CP na Legas ya bayar da umarnin tsige DPO na ofishin ‘yan sanda na Meiran cikin gaggawa.

Hundeyin ya rubuta, “CP Idowu Owohunwa ya ba da umarnin a tsige DPO Meiran nan take saboda rashin adalci da kuma rashin bin doka da oda.

“A halin da ake ciki, an gano dukkan jami’an da abin ya shafa kuma a halin yanzu suna hedikwatar rundunar inda aka fara bincike akansu.”

Leave a Reply