Kwamishinan Sufuri na Kano ya karɓi cin hancin Dala Dubu 30 kan karɓar belin dillalin miyagun ƙwayoyi

0
321
Kwamishinan Sufuri na Kano ya karɓi cin hancin Dala Dubu 30 kan karɓar belin dillalin miyagun ƙwayoyi
Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Namadi

Kwamishinan Sufuri na Kano ya karɓi cin hancin Dala Dubu 30 kan karɓar belin dillalin miyagun ƙwayoyi

Daga Jameel Lawan Yakasai

Wasu majiyoyi daga hedikwatar hukumar DSS da ke Abuja, sun shaida wa jaridar Daily Nigerian cewa, hukumar ta yi binciken sirri, kan zargin kwamishinan sufuri na Kano Ibrahim Namadi Dala, da karbar cin hanci, kafin ya karbin belin babban dilan ƙwaya Ibrahim Ɗanwawu.

Haka kuma hukumar ta DSS ta mika rahoton ga gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ta bada shawarar korar kwamishinan daga mukaminsa.

KU KUMA KARANTA: Ƙungiyar Lauyoyi a Kano, ta nemi Kwamishinan Sufuri ya bayyana waɗanda suka saka shi ya yi belin dilan ƙwayoyi

Rahotanni sun nuna cewa tun da farko gwamna Abba Yusuf yayi niyar korar kwamishinan nan take, amma bayan ya yi shawara da jagoran jam’iyyar NNPP Sanata Rabiu Kwankwaso, sai ya fasa yin hakan.

Tuni dai gwamna Abba Kabir Yusuf ya kafa kwamitin bincike kan lamarin, tare da umartar kwamitin ya mika rahoto cikin mako guda.

Leave a Reply