Kwale-kwale ya kama da wuta a Neja, yara biyu sun mutu

0
151

An tabbatar da mutuwar wasu yara biyu sakamakon gobarar kwale-kwale a ƙaramar hukumar Katcha ta jihar Neja.

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Salihu Garba, ya ce kwale-kwalen ya kama wuta ne biyo bayan wata matsala da injin ya samu, wanda ya sa wata jarkan man fetur ya kama wuta.

Garba ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6 na yammacin ranar Juma’a, 20 ga watan Oktoba, kuma jirgin na ɗauke da fasinjoji 145.

KU KUMA KARANTA: Mutum 40 a Kebbi sun ɓace bayan kifewar kwale-kwale

Yace; “NSEMA ta samu rahoton wani hatsarin kwale-kwale da ya yi sanadin mutuwar yara biyu tare da raunata mutane biyu a ƙaramar hukumar Katcha.  Lamarin dai ya faru ne ranar 20/10/2023 da misalin ƙarfe 6 na yamma inda injin kwale-kwalen ya kama wuta kuma ya sa man fetur da aka ajiye a cikin wata jarka a jirgin da ke ɗauke da mutane 145 ya kama wuta.

“Mutanen ’yan ƙabilar Danbo ne a Jihar Kogi, suna kan hanyarsu ta dawowa daga Kasuwar Katcha.  Ya zuwa yanzu dai an gano gawar ɗaya yayin da ake ci gaba da neman na biyun.”

Leave a Reply