Wani rahoto da Ƙungiyar Tarayyar Turai ta fitar, ya tabbatar da cewa kusan mutum 400,000 ne suka mutu a nahiyar Turai, sakamakon shaƙar gurɓatacciyar iska.
Rahoton, ya nuna cewa wannan ibtila’I ya faru ne a shekarar 2021 kaɗai, tare da cewar da an bi dokokin da WHO ta gindaya, da addadin basu kai haka ba.
Hukumar kula da muhalli ta Turai, ta ce a tsakanin ƙasashen Turai kaɗai, gurɓatacciyar iskar da ke shafar mutanen da ke fama da ciwon zuciya, ta yi sanadin mutuwar mutum 253,000 a shekarar 2021 kaɗai.
Gurbatacciyar iskar da ake samu daga sinadarin nitrogen dioxide ko kuma NO2, ta fi shafar mutanen da ke fama da ciwon sukari, inda ta kashe mutum 52,000.
KU KUMA KARANTA: Guguwar iska ta lalata gonakin kaji, ta kashe tsuntsaye dubu uku a Filato
Idan aka haɗa da ƙasashen da ke wajen Turai kuwa, EU ta ce, adadin ya kai 389,000 na waɗanda suka mutu, sakamakon nau’in iskar nitrogen dioxide NO3
A cewar rahoton, dole ne a ɗauki matakan kariya, idan har ana son kawo ƙarshen mace-macen mutanen da ke shakar wannan iska mai haɗarin gaske, musamman a ƙasashe mambobin Ƙungiyar Tarayyar Turai.