Sama da mutum 90,000, wato kusan kashi 4 cikin 100 na al’ummar Gaza a halin yanzu ko dai sun mutu ko sun samu rauni ko sun ɓace, kamar yadda wata ƙungiyar kare hakkin bil adama ta bayyana.
Ƙungiyar Euro-Mediterranean Human Rights Monitor ta bayyana haka ne bayan binciken da ta yi dangane da irin hare-haren ta sama da ƙasa da ruwa da ke ci gaba da kaiwa a Gaza waɗanda suka lalata kaso 70 cikin 100 na ababen more rayuwa a birnin.
Ƙungiyar ta zargi Isra’ila da mayar da Zirin Gaza wurin da ba zaman lafiya.
Ɗaruruwan gawarwakin da ba za a iya ɗaukarsu ba sun kasance a kan tituna, a cewar ƙungiyar, musamman a yankunan da sojojin Isra’ila suka kai farmaki ta ƙasa.