Kurame sun buƙaci a gina musu makarantar kwana a Damaturu

0
145

Ƙungiyar Kurame Musulmi a Najeriya (ADMUN) ta roƙi gwamnatin Yobe da ta tarayya da su gina makarantar musamman ta kurame a Damaturu, babban birnin jihar.

Mataimakin shugaban ƙungiyar, Mohammed Abubakar Sadiq ne ya yi wannan ƙiran a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida game da taron da’awa na shekara-shekara karo na 32 da kuma taron kurame na ƙasa a Najeriya da suke gudanarwa a Damaturu.

Taron mai taken, “Ƙalubalen da ake fuskanta a rayuwar kurame Musulmi ” na gudana ne a Kwalejin ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Damaturu.

KU KUMA KARANTA: Kano da Bauchi sun lashe gasar Alƙur’ani ta ƙasa ta 2023

Sadiq ya ce makasudin da’awar da shirye-shiryen taron “shi ne yaɗa ilimin addinin Musulunci a faɗin Najeriya.”

Ya buƙaci jama’a da su sani cewa ƙungiyar “tana gudanar da tarukanta a duk shekara” kuma akwai ƙalubale da dama da suke fuskanta musamman a ɓangaren samar da kuɗaɗe.

“Mutane da yawa sun yi alƙawarin taimaka mana, amma sun kasa cika alƙawurran da suka ɗauka.

“Don haka ina ƙira ga gwamnati ta duba mu domin mu ga ƙarshen waɗannan matsalioli cikin nasara.

“Sauran ƙalubalen da muke fuskanta shi ne ta fannin ilimi; mun ba da shawarar gina mama makarantar kwana a babban birnin jihar Yobe kana kurame ba su da wani aiki kuma har yanzu ba a yi komai ba ta fuskar taimako,” inji shi.

Leave a Reply