Ku guji yin rikici da sunan addini — Shaikh Zakzaky ya faɗa wa Musulmi da Kiristoci da suka kai masa ziyara a Abuja
Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya karɓi baƙuncin wakilan al’ummar Unguwar Nasarawa da ke Kaduna, a wata ziyara ta musamman da ta ƙunshi manyan shugabannin addinai daga ɓangarorin Musulmi da Kiristoci.
Cikin tawagar akwai Mista Zakari, wakilin ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) a ƙaramar hukumar Chikun, Alhaji Aliyu Mai Lafiya Chiroman Nasarawa, Mista Dominic, babban faston cocin Katolika na Unguwar Nasarawa, da Shaikh Alaramma Jabir Muhammad, babban limamin masallacin Juma’a na yankin.

A yayin ganawar wacce ta kasance a ranar Talata 13 ga Jimada Ula, 1447, daidai da 4 ga watan Nuwamban 2025 wacce Ofishin Shehin Malamin ya labarta, Jagora Shaikh Zakzaky (H) ya yi kira mai ƙarfi ga al’umma da su guji kowacce irin fitina ko rikici da za ta iya kawo rabuwar kai tsakanin Musulmi da Kiristoci.
KU KUMA KARANTA: Shaikh Zakzaky ya raba kayayyakin abinci ga mabuƙata a Zariya
Ya ce, “Kar ku yarda a haɗa ku rigima da juna, ko da da sunan addini ko da da sunan ƙabila. Ku zauna lafiya, ku haɗa kai domin amfanin kowa da kowa.”

Jagoran ya bayyana cewa Kiristoci ba arna ba ne, yana mai tunatar da cewa Allah Maɗaukaki ya ambace su a cikin Alƙur’ani da suna “Ma’abota Littafi”. Ya ce wannan dalili ne da ya wajabta a ci gaba da girmama juna da ƙarfafa zumunci da fahimtar juna a tsakanin mabiya addinan.
Wannan ganawa ta kasance wata dama ta ƙarfafa haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin shugabannin addinai a Nasarawa, abin da da dama suka yaba da shi a matsayin mataki mai muhimmanci wajen gina zaman lafiya da haɗin kai a Kaduna da ma kasar baki ɗaya.









