Ku buɗe shagunanku ko mu ƙwace – Gwamna Yobe ya gargaɗi ‘yan sabuwar kasuwar Damaturu

0
154
Ku buɗe shagunanku ko mu ƙwace - Gwamna Yobe ya gargaɗi 'yan sabuwar kasuwar Damaturu
Gwamnan Yobe, Dakta Mai Mala Buni

Ku buɗe shagunanku ko mu ƙwace – Gwamna Yobe ya gargaɗi ‘yan sabuwar kasuwar Damaturu

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, CON, ya yi gargaɗi ga ’yan kasuwar da aka raba musu shaguna a Kasuwar Zamani ta Ibrahim Gaidam, Damaturu, cewa duk wanda bai bude shagonsa ba ko kuma ya gaza amfani da shi yadda ya kamata, gwamnati za ta kwace shagon ta ba wa wani.

Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne yau a Filin Wasanni na 27 ga Agusta, Damaturu, yayin kaddamar da rabon buhunan hatsi 50,000 ga al’ummomin da ke cikin mawuyacin hali a faɗin jihar, a ƙarƙashin Shirin Tallafin Abinci na Gwamna Buni na 2025.

Ya bayyana rashin jin daɗinsa kan halin wasu masu shaguna da suka rufe shagunan da aka ba su maimakon su yi amfani da su, lamarin da ya ce yana hana sauran ’yan kasuwa da ke son gudanar da sana’a damar cin gajiyar kasuwar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Yobe zai ƙaddamar da sabon shirin tallafin noma na bana (Hotuna)

Gwamna Buni ya umurci Ma’aikatar Kasuwanci ta jihar da ta gaggauta aiwatar da umarnin domin tabbatar da cewa dukkan shagunan da aka raba an buɗe su kuma ana amfani da su yadda ya dace.

“Ba za mu yarda gwamnati ta zuba jari wajen gina irin wannan kasuwar zamani ba, sai a bar shaguna a rufe. Duk wanda aka ba shi shago amma ya ƙi amfani da shi, gwamnati za ta kwace ta kuma ba wa wani da ke da niyyar yin kasuwanci. Wadanda suke tunanin za su ci gaba da riƙe shago a rufe, suna wasa ne—ba za mu lamunta da haka ba,” in ji gwamnan.

Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakai don inganta harkokin kasuwanci, ƙirƙirar ayyukan yi, da kuma ƙara ƙarfin tattalin arzikin jihar ta hanyar samar da ingantattun cibiyoyin kasuwanci kamar Kasuwar Zamani ta Ibrahim Gaidam.

Leave a Reply