Ku ba mu dama mu kakkaɓe ‘yan ta’adda – sojojin Najeriya ga gwamnonin arewa

1
286

Rundunar sojin Najeriya ta yi ƙira ga gwamnonin yankin Arewa da su bai wa sojojin dama domin kawar da ‘yan ta’adda.

Babban hafsan sojin ƙasa, Taoreed Lagbaja ne ya yi wannan roƙo a hedikwatar rundunar da ke Abuja a lokacin da yake karɓar baƙuncin gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal.

Yayin da yake kawar da yiwuwar yin afuwa ga ‘yan fashin da ke addabar yankin Arewa maso yammacin ƙasar nan, Mista Lagbaja ya gargaɗi masu laifin da su fice daga ƙasar nan take.

Bayanin hafsan sojin ya biyo bayan ƙiraye-ƙirayen da tsohon gwamnan jihar, Sani Yerima ya yi a kwanakin baya na cewa a yi wa ‘yan bindigar afuwa.

A cewarsa, Sojoji ba za su bari su shiga wasu sassan ƙasar ba.

KU KUMA KARANTA: Rundunar sojin saman Najeriya ta sake naɗa manyan hafsoshi 98 ​

“Mai girma gwamna, ina ganin muna buƙatar mu duba wannan shirin na afuwa.

Abubuwan da ke aikata laifuka sun tabbatar da cewa ba za a iya gyara su ba.

Don haka, batun yin afuwa ya samar da hanyar da za su sake haɗuwa su sake shiryawa da ƙaddamar da hare-hare,” in ji Mista Lagbaja.

1 COMMENT

Leave a Reply