Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da Gawuna a matsayin gwamnan Kano

0
240

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja babban birnin Nijeriya ta tabbatar da Nasiru Yusuf Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin halastaccen gwamnan Kano a zaɓen watan Fabrairun 2023.

Kotun ta kuma buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP ya mika mulki ga Gawuna.

Ta bayyana haka ne a hukuncin da ta yanke ranar Juma’a.

Kotun ta tabbatar da hukuncin da kotun sauraren ƙararrakin zaɓe ta jihar Kano ƙarkashin jagorancin Mai Shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ta yanke wanda ya sauke Abba Kabir Yusuf daga mukamin gwamnan jihar ranar 20 ga watan Satumba.

Kotun ta cire ƙuri’a 165,663 daga ƙuri’un da Abba Gida-Gida ya samu inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a manna wa ƙuri’un 165,663 hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.

KU KUMA KARANTA: An baza ƙarin sojoji da ‘yan sanda a Kano gabanin hukuncin kotu kan shari’ar Abba da Gawuna

Sai dai jim kaɗan bayan hakan, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya shigar da ƙara inda yake kalubalantar hukuncin kotun.

Tun da farko a zaɓen da aka yi a watan Maris ɗin 2023 Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya samu kuri’u 1,019,602, sai kuma Nasiru Yusuf Gawuna na APC ya samu 890,705.

Leave a Reply