No menu items!

Sample Page Title

Date:

Daga Ibraheem El-Tafsser

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP, a zaɓen gwamnan jihar Kano na 2023.

Mai shari’a John Okoro wanda ya karanta hukuncin ya ce kotun ɗaukaka ƙara ta yi kuskure wajen tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar, wadda ta ce Abba Kabir bai samu rinjayen ƙuri’u a zaɓen watan Maris ba.

Saboda haka, kotun ta yi kuskure wajen zabtare wa Abba da NNPP ƙuri’u.

A game da batun rashin kasancewar Abba Kabir ɗan jam’iyyar NNPP, kotun ta ce jam’iyya ce kawai take da ikon tantance ɗanta ko wanda ba ɗanta ba.

Saboda haka ne kotun ta amince da ɗaukaka ƙarar jam’iyyar NNPP, tare da yin watsi da hukunce-hukuncen kotun ɗaukaka ƙara da kuma na kotun sauraron ƙorafin zaɓen Kano.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya bayyana kyautar N35,000 ga ma’aikata da ‘yan fansho a jihar

Wannan shi ne matakin ƙarshe a turka-turkar shari’a da aka kwashe tsawon watanni ana yi, game da sahihancin sakamakon zaɓen gwamnan Kano.

Tun da farko, kotun zaɓen gwamnan Kano a watan Satumban 2023 ce ta soke ƙuri’a 165,633 wadda in ji ta, aka yi wa ɗan takarar na jam’iyyar NNPP aringizo, bayan hukumar zaɓe a watan Maris, ta ce ya samu ƙuri’a 1,019, 602.

Gwamna Abba dai bai gamsu da hukuncin ba, don haka ya wuce zuwa kotun ɗaukaka ƙara.

Sai dai, ita ma kotun ɗaukaka ƙarar ta bai wa jam’iyyar APC nasara bisa hujjar cewa Abba ba ɗan jam’iyyar NNPP ba ne lokacin da aka tsayar da shi takara, don haka ta nemi a rantsar da ɗan takararta Nasiru Gawuna.

A ranar 20 ga watan Maris na 2023 ne Hukumar zaɓen Najeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan na jihar Kano.

Babban jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim ya bayyana cewa Abba Kabir ya samu ƙuri’u 1,019,602, yayin da Nasiru Gawuna ya samu ƙuri’u 890,705.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...